Tsohon shugaban ya samu kyakyawar tarbo daga daruruwan magoya bayan ‘yan republican a Jihar South Carolina inda mutanen Jihar ke daukarsa da kima.
Bush ya bayyana kanin shi a matsayin wanda ya fi dacewa ya jagoran ci kasar a wannan lokaci.
Jeb Bush dai ya kashi a zaben fitar da gwani na Republican da aka gudanar a Jihohin Iowa da New Hampshire.
North Carolina ce Jiha ta uku da za a yi zaben fitar da gwanin wanda zai jagoranci Republican ga nasara a zaben shugaban kasa na 2016.